play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Cin Zarafi
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right An Tsare Magidancin Da Ya Yi Wa Agolarsa Fyade A Kurkuku

Cin Zarafi

An Tsare Magidancin Da Ya Yi Wa Agolarsa Fyade A Kurkuku

Bello Sani February 18, 2021 7


Background
share close

Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari bisa zargin sa da yi wa agolarsa mai shekara 14 fyade.

Babbar Kotun Majistaren ta ba da umarnin a tsare mahaucin mai shekara 40 ne bayan an gurfanar da shi a gabanta kan lalata karamar yarinyar.

Babban alkalin kotun, P.E. Nwaka ya ba da umarnin a tsare magidancina a gidan yarin da ke Ikoyi a jihar Legas, sannan ya dage sauraron karar har sai ranar 18 ga watan Fabrairu.

Tun da farko, lauya mai shigar da kara, ASP Thomas Nurudeen ya fada wa kotun cewa mutumin ya aikata laifin ne a watan Janairu a unguwar Ilasamaja da ke Legas.

Nurudeen ta ce yarinyar ta fada wa mai ba ta shawara a makaranta ne cewa mahaifin na ta ya lalata ta.

Ya ce mai ba ta shawara ta kai karar lamarin ga ma’aikatar matasa da ci gaban zamantakewar jihar Legas wacce ta kai ta ga ‘yan sanda.

Mai Shari’a Nwaka ya yi watsi da hanzarin magidancin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

Laifin, in ji shi, ya ci karo da sashi na 137 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas, ta shekarar 2015.

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *