play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right An samu rabuwar kai tsakanin ‘yan majalisar Najeriya kan sake bude makarantu

Labarai

An samu rabuwar kai tsakanin ‘yan majalisar Najeriya kan sake bude makarantu

Bello Sani January 18, 2021 10


Background
share close

A Najeriya an samu rabuwar kai tsakanin ‘yan majalisar dokokin kasar game da batun sake komawa makarantu a yau Litinin a ƙasar.

A ranar Alhamis ne ma’aikatar ilmi ta tarayya ta sanar da cewa, gwamnatin ƙasar ta amince a koma makarantu ranar 18 ga watan Janairu, kamar yadda aka tsara tun da farko.

Sai dai jiya, rahotanni sun ambato kwamitin majalisar wakilai kan ilmi a matakin farko na nuna adawa da sake buɗe azuzuwa a lokacin da aka ambata.

To sai dai shugaban kwamitin ilmi mai zurfi na majalisar wakilan Aminu Sulaiman Goro, ya ce wannan ba matsayin majalisarsu ba ne.

“Kamar yadda ka sani a yanzu majalisa tana dogon hutu kuma sai nan da mako guda za mu koma. Saboda haka ba majalisa ce ta dauki wannan mataki ba.”

Sai dai ya ce tabbas ra’ayoyin ‘yan majalisar kamar na sauran ‘yan kasa ya rabu “inda wasu ke ganin bai kamata a koma makarantun ba a bisa la’akari da yadda annobar korona ke karuwa a duniya to amma akwai da yawa daga cikinmu da ke ganin komawar ta yi dai-dai bisa ala’akari da yadda dalibai suka yi asarar kusan shekara guda.”

Kwamared Aminu Goro ya ce ma’aikatar ilimi ta kasa ta sanar da majalisar batun sake bude makarantun ” kuma suna da ikon yin hakan.”

“Sai dai nan gaba idan muka ga akwai wata illa dangane da komawar ko kuma jama’a suka gano illar, to a lokacin ne mu ‘yan majalisa za mu dauki mataki.”

Komen da annobar korona dai ta yi ne ya sa gwamnatin Najeriya ta bi sawun wasu kasashen duniya wajen sake rufe makarantu domin gudun yaduwar cutar.

A watan Satumbar 2020 ne dai makarantu a Najeriya suka sake budewa bayan kwashe kusan watanni shida suka rufe sakamakon annobar korona.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *