play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

Kiwon Lafiya

An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

Bello Sani April 10, 2021 8


Background
share close

Bayan zaman awanni takwas da gwamnatin tarayya ranar Juma’a, da yiwuwan kungiyar Likitoci NARD za ta janye yajin aikin a yau Asabar.

A cewar ThePunch, an samu labari daga ganawar da suka yi tun daga karfe 3 na rana zuwa 11 na dare ranar Juma’a cewa bangarorin biyu sun samu matsaya kuma sun rattafa hannayensu kan yarjejeniya.

Wata majiya ta ce Likitocin sun amince zasu janye yajin aikin da aka kwashe kwanaki tara yanzu anayi idan shugabannin kungiyarsu suka amince.

Wakilan Likitocin sun yi alkawarin ganawa da mambobinsu ranar Asabar, sannan su yanke shawara.

“An samu matsaya a ganawar kuma Likitocin sun amince da abubuwan da akayi na amsa bukatunsu. Saboda haka za su gana da mambobinsu ranar Asabar kuma su yanke shawara kan yajin aikin,” majiyar tace.

Da farko, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi iyakan kokarinta wajen amsa bukatun Likitocin guda bakwai.

Hakazalika kwamitin kiwon lafiya na majalisar wakilai ta zanna da Likitocin don rokonsu su janye yajin aiki don rayuwar talakawan dake kwance a asibitocin gwamnatin kuma ba za su iya zuwa na kudi ba.

Shugaban kwamitin, Tanko Sununu, yayin hira da manema labarai bayan zaman ya ce Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, zai gana da Likitocin ranar Talata.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *