
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da sace yara shida, ‘ya’ya ga Alhaji Sani Gyare da ke kauyen Kadauri a karamar hukumar Maru.
Kakakin rundunar, SP Shehu Muhammed ne ya tabbatarwa da kamfanin dillacin labaran Najeriya – NAN a birnin Gusau.
A cewarsa, ‘yan sanda sun samu labarin sace yara bakwai, shida a gidan Alhaji Gyare sai kuma yarinya ta bakwai a gidan wani makwabcinsa duk a kauyen Kadauri.
“Kwamishinan ‘yan sanda, CP Abutu Yaro ya tura runduna ta musamman domin ceto yaran,” in ji kakakin ‘yan sandan.
Bayanai sun nuna cewa masu garkuwa da mutane sun isa kauyen ne a ranar Juma’a da daddare inda suka aikata wannan mummunan aikin.
Sace mutane domin karbar kudin fasa na kara yawaita a jihohin arewa maso yammacin Najeriya musamman jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)