play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right An kori ma’aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda

Labarai

An kori ma’aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda

Bello Sani February 10, 2021 5


Background
share close

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta kori sabbin ma’aikatan da ta dauka su fiye da arba’in da biyu bayan sun shafe shekara guda babu albashi.

Daily Nigerian ta rawaito cewa na dauki sabbin ma’aikatan ne a watan Disambar shekarar 2019, watanni kalilan kafin a cire tsohon shugaban NEMA, Mustapha Maihaja.

Sabbin ma’aikatan sun samu rubutaccen sakon sanar da su janye aikin da aka daukesu a yayin da suke jiran sakon wuraren da za’a tura domin fara aiki a karkashin sabon shugaban NEMA, AVM Muhammadu Mohammed.

A cikin sakaon da ta aike musu, NEMA ta sanar da sabbin ma’aikatan cewa an daukesu aiki ne ba bisa ka’ida ba, saboda ba’a bi ka’idojin da ya kamata ba kafin daukan sabbin ma’aikata.

An fara aikawa sabbin ma’aikatan sako a cikin watan Yuni na shekarar 2020, inda aka sanar da su cewa su dan dakata har zuwa lokacin da za’a kammala bincike akan daukansu aiki.

A sako na biyu da aka aika musu a ranar 25 ga watan Janairu, 2021, NEMA ta sanar da sabbin ma’aikatan cewa sakamakon bincike ya nuna cewa ba’a daukesu aiki bisa ka’ida ba.

Takardar sakon, mai dauke da sa hannun Musa Zakari, mataimaki darekta a NEMA, ta sanar da sabbin ma’aikatan cewa an soke batun daukansu aiki.

Sai dai, sabbin ma’aikatan, wadanda suka ajiye wasu ayyukansu domin komawa NEMA, sun kafe akan cewa sun bi duk wasu matakai da ya kamata kafin a kai ga daukansu aiki.

Ma’aikatan da ka sallama sun bayyana cewa hukumar NEMA ba ta taba basu ko sisi ba a matsayin albashi tun bayan daukansu aiki da kammala bude musu fayil a matsayin sabbin ma’aikata.

Sabbin ma’aikatan sun dora alhakin sallamarsu akan tsofin ma’aikatan NEMA wadanda tun farko suka nuna musu kuru-kuru cewa basa kaunar ganinsu a hukumar.

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *