Rundunar yan sanda ta sanar da rasa wani jami’inta sakamakon wata zanga-zangar yan shi’a a Abuja. Lamarin ya afku ne a ranar 7 ga watan Mayu wanda yayi daidai da tattakin da suke yi a ran Juma’ar karshe ta Ramadan

An kuma yi nasarar cafke ‘ya’yan kungiyar guda 49, sannan za a gurfanar da su da zaran an kammala bincike.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kisan wani jami’inta, ASP Adama Ezekiel, yayin wata zanga-zangar da ‘yan kungiyar shi’a (IMN) suka yi.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar FCT, Mariam Yusuf, mataimakiyar Sufeta ta ’yan sanda, ce ta sanar da mutuwar Ezekiel a cikin wata sanarwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Leave a Comment

%d bloggers like this: