Rundunar ƴan sandan jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama mutum 11 da ake zarginsu da hannu a yi wa wata mata mai shekara 50 dukan da ya yi sanadin mutuwarta a gidan Sarkin Kano, bisa zargin maita.

Ta ce ta kama wadanda ake zargin ne a ranar Talatar da ta wuce bayan samun labarin faruwar al’amarin, sannan tana ci gaba da neman ƙarin wasu mutanen da ake zarginsu da hannu a faruwar al’amarin.

Da yake yi wa BBC karin bayani, kakakin rundunar ƴan sandan a Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce al’amarin ya faru ne a ranar Asabar ɗin makon da ya gabata. Tuni dai aka yi jana’izarta.

Ya ce wasu daga cikin dogarawan Sarkin Kano ne suka lakaɗa wa wata mata duka bisa zargin ita mayya ce, kuma ta kama wata yarinya da ke sashen ɗaya daga cikin matan marigayi Sarkin Kano Ado Bayero.

Ya ce: “Mun fara samun bayanin ne ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata. Binciken namu ya nuna tun ranar Asabar abin ya faru.

“Kuma lokacin da batun ya zo mana ma har an binne matar. Mu kuma muka ga akwai buƙatar bincike. Har yanzu muna gudanar da binciken amma ba mu kammala ba.

“Da farko mun fara samun mutum biyu, daga baya muka sake samun mutum tara, maza shida mata uku. Akwai wadanda muke nema kuma in shaa Allah za mu kama su.

DSP Kiyawa ya ce idan an kammala bincike za su shaida wa manema labarai sakamakon binciken.

Sai dai rundunar ƴan sandan jihar ba ta kai ga faɗar sunan matar da kuma garin da ta fito ba.

Amma wani bincike da wakilin BBC Khalifa Dokaji ya gudanar ya nuna cewar matar ƴar asalin ƙaramar hukumar Warawa ce da ke arewacin jihar ta Kano.

Sai dai BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban ma’aikatan fadar Sarkin Kano, Alhaji Ahmad Ado Bayero, sai dai bai amsa wayar ba da kuma gajeren saƙon da wakilinmu ya aika masa.

A farkon makon da muke ciki ne dai rahotanni suka fara bayyana cewar daya daga cikin ƴaƴan marigayi Ado Bayero, ta zargi matar da cewar mayya ce saboda ta kama wata yarinya da ke gidan.

Sai ta umarci wasu daga ciki dogaran da ke cikin gidan Sarkin Kano su yi wa matar dukan tsiya, da zummar sai ta amsa zargin da ake yi mata.

Wannan batu dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake shirye-shiryen fara shagulgulan bai wa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sandar mulki, wanda gwamnan Kano zai yi a ranar Asabar 3 ga watan Yuli.

Leave a Comment

%d bloggers like this: