play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Shariah
  • keyboard_arrow_right An Gurfarnar Da Shi A Gaban Kotu Saboda Taurin Bashi

Labarai

An Gurfarnar Da Shi A Gaban Kotu Saboda Taurin Bashi

Bello Sani February 19, 2021 6


Background
share close

An gurfanar da wani matashi mai kimanin shekaru 28 a gaban wata kotun Majistare ranar Alhamis bisa zargin taurin bashin kudi har N600,000.

Ana dai tuhumar matashin ne da laifuka biyu, duk da cewa ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.

Dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, Kayode Adeoye, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar uku ga watan Febarairun 2021 a unguwar Owoeba dake Karamar Hukumar Oshogbo.
Yace wanda ake tuhumar ya ranci kudaden a hannun wani mai suna Obisesan Olalekan, bisa alkawarin zai dawo masa da kudadensa amma ya gaza yin hakan.
Dan sanda ya ci gaba da cewa, aikata wannan laifin ya saba da sassa na 419 da 383 na Kundin Dokoki na Jihar Osun.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai shari’a Isola Omisade, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N500,000, da kawo mutane biyu da za su tsaya masa.

Alkalin ya kuma ce cikin mutane biyun da za su tsaya masa, dole daya daga ciki ya kasance ma’aikacin gwamnati, dayan kuma ya kasance dan uwansa na jini.

Dagan an sai ya dage zaman kotun zuwa ranar 22 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *