
Wani tsohon injiniya a kamfanin Amazon ya ƙaddamar da wata manhaja da za ta riƙa fassara kukan mage.
Manhajar mai suna MeowTalk tana naɗar sauti sannan ta yi yunƙurin fahimtar ma’anarsa.
Mutumin da ya mallaki kyanwar zai taimaka wajen fassara kukan, abin da zai bai wa manhajar damar koyon yadda ake yin fassarar.
A halin yanzu, jimloli 13 akwai aka fassara a cikin manhajar waɗanda suka haɗa da: “A ba ni abinci!”, “Ina jin yunwa!” da kuma “Ku bar ni!”
Bincike ya nuna cewa maguna ba su da yare kamar yadda ɗan adam yake da shi.
Kukan kowacce mage ya sha bamban da na ƴar uwarta kuma tana yin sa ne bisa alaƙarta da mai ita, sannan wata ta fi wata kuka.
Don haka a maimakon tattara kowaɗanne irin bayanai na kukan maguna, fassarar manhaja za ta ta’allaƙa ne kan kowace mage daban.
Ta hanyar naɗar kukan, manhajar basirar na’ura da wani injin daban mai manhajar koyo ne za su fi fahimtar
Ta hanyar naɗar sauyin da alamta sautin, ilimin da manhajar suna iya fahimtar muryar ko wace irin mage – duk lokacin da aka yi amfani da shi, zai iya zama daidai.
Manufar ita ce a samar da basirar fahimta, kamar yadda Javier Sanchez, manajan shiryawa na kamfanin samar da manhaja na Akvelon, ya fada a shafin kamfanin na intanet.
Nan take fasahar za ta fassara kukan magen, sai a ji muryan mutum.
Post comments (0)