play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Cin Zarafi
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Amnesty ta zargi sojojin Eritrea da kashe daruruwan fararen hula a Tigray

Cin Zarafi

Amnesty ta zargi sojojin Eritrea da kashe daruruwan fararen hula a Tigray

Bello Sani March 1, 2021 5


Background
share close

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International tace dakarun Etritrea sun yiwa daruruwan fararen hula kisan gilla a Tigray mai fama da rikicin ‘yan tawayen TPLF, yankin da suka yi iyaka da shi daga bangaren arewacin Habasha.

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Juma’a 26 ga watan Fabarairu, Amnesty ta bayyana kisan gillar a matsayin ta’asa babba da ka iya zama laifin yaki.

Amnesty tace ta tattara hujjojinta ne bayan ganawa da wasu daga cikin fararen hular da suka tsira daga kisan gillar dakarun kasar ta Eritrea su 41, sai kuma hotunan da ta samu daga tauraron dan adam, wadanda suka nuna yankunan da aka tafka mummunar ta’asar.

Sai dai ministan yada labaran Eritrea Yemane Gebremeskel yayi watsi da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin yunkuri na shafawa kasarsa kashin kaji.

Tun cikin watan Nuwamba ake gwabza fada tsakanin sojojin Habasha da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray, bayan da Fira Minista Abiy Ahmad ya bada umarnin afka musu, bayan da suka kaddamar da farmaki kan sansanonin sojojin kasar.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *