Mai dakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta rufe shafinta na Twitter jim kadan bayan sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta dakatar da shafin a Najeriya a yammacin ranar Juma’a.

“Zan rufe shafina na Twitter a yanzu. Fatan alheri ga Najeriya,” kamar yadda ta rubuta gabanin rufe shafin.

Zuwa shafiyar ranar Asabar mafi yawan masu amfani da shafin na Twitter ba sa samun damar shiga, sai dai ta wata manhajar intanet mai suna VPN.

Dan haka ko sun sanya wani abu a shafin nasu zai zama ya fita da sunan wata kasar daban ba Najeriya ba.

Tun da farko sai da Ministan yada labaran kasar Ali Mohammed ya yi zargin kamfanin Twitter baya tafiyar da abubuwansa bisa gaskiya a Najeriya, ya kara da cewa shi yasa gwamnati ta yanke hukunci ta dakatar da shi.

Wannan dai duka na zuwa ne kwana biyu bayan da Twitter ya goge wani bayani da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi, wanda yake gani ya saba ka’idojinsa.

Leave a Comment

%d bloggers like this: