play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right A karo na biyu Tattalin arziƙin Najeriya ya sake faɗawa cikin mawuyacin hali

Siyasa

A karo na biyu Tattalin arziƙin Najeriya ya sake faɗawa cikin mawuyacin hali

Bello Sani November 22, 2020 7


Background
share close

Najeriya ta fada cikin matsin tatalin arziki a karo na biyu cikin shekaru 5 sakamakon annobar Covid 19 da faduwar farashin danyen mai, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar nan ta bayyana a jiya Asabar.

Kudaden shigar da kasar nan ta ke samu a cikin rubu’i na 3 na wannan shekarar ya yi kasa a karo na 2 a jere, da kashi 3 da digo 62, a cewar hukumar kididdiga ta NBS.

Hukumar ta NBS ta dora alhakin haka a kan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma tasirin annobar coronavirus.

Kudaden shiga da ke da nasaba da danyen mai ya yi kasa da kusan kashi 14, idan aka kwatanta da kusan kashi 7 a rubu’i na 2, a cewar hukumar.

Asusun ba da lamuni na duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar nan zai rikito da sama da kashi 5 a wannan shekarar, amma gwamnatin tarayya ta ce zai fadi da kusan kashi 9.

Najeriya, wacce ita ta fi samar da danyen mai a nahiyar Afrika, kafin yanzu, tana samar da ganga miliyan 2 ne duk rana, amma tasirin annobar covid 19 ya sa ta sauka zuwa ganga miliyan 1 da dubu dari 4.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *