Jita-jita na yawo cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai bar jam’iyyar adawa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai jin dadin irin zaman da ake yi a PDP Idan ta tabbata, tsohon Ministan zai iya komawa APCn da ya baro a 2018 Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kusa karkare shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP, inda ake tunani zai koma APC.

Politics Digest ta fitar da rahoto cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai jin dadin zamansa a PDP, don haka ya ke harin ya koma APC mai mulki da ya baro. Rabiu Kwankwaso wanda ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya tattauna da shugaban riko na APC, gwamna Mai Mala Buni.

Daga cikin wadanda su ke kokarin dawo da Rabiu Kwankwaso tafiyar APC akwai gwamna Badaru Abubakar da Muhammad Bello Matawalle wanda ya bar PDP.

Sauya-sheka za ta raba kan ‘Yan Kwankwasiyya da APC Idan hakan ta tabbata, ana tunani Kwankwaso zai bar PDP tare da wasu manyan yaransa irinsu Injiniya Abba Kabir Yusuf da Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo. Amma wasu daga cikin ‘Yan Kwankwasiyya ba za su sauya-sheka zuwa jam’iyyar ta APC ba. Kwamishinan raya karkara na Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce su na murna da wannan lamari, amma ya gargadi tsohon gwamnan a kan kawo rikici a APC.

Leave a Comment

%d bloggers like this: