
Hukumar bunkasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su fara aiki a ƙasashen ƙetare ta hanyar Intanet, kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta rawaito
“Akwai tsarin da mu ka fitar a kwanan nan wanda ƴan ƙasa za su ci gajiyarsa. Tsari ne wanda za su iya samun aiki a wata ƙasa su kuma gabatar da shi alhalin su na nan Najeriya wajen amfani da yanar gizo.
Mun zo da wannan tsarin ne saboda mun ga kamar ƙasar Indiya ce ta mamaye wannan bangaren kasuwanci a Duniya, sai mu ka ga ai Najeriya mun ma fi ƙasar Indiya dama idan za a yi.
Na farko, lokacin mu ya fi kusa da ƙasar Amurka da Turai akan lokacin Indiya. Na biyu, Najeriya mun fi mutanen da su ka iya turanci, saboda yanzu a ƙasar Indiya wadanda su ka iya turancin ma raguwa su ke, saboda haka muka fitar da tsarin yadda Najeriya za ta mori wannan tsari”.
Post comments (0)