play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Ƙungiyar ƴan Shi’a ta Zakzaky ta soki gwamnatin Kano kan Sheikh Abduljabbar

Siyasa

Ƙungiyar ƴan Shi’a ta Zakzaky ta soki gwamnatin Kano kan Sheikh Abduljabbar

Bello Sani February 8, 2021 65


Background
share close

Ƙungiyar IMN ta ƴan shi’a mabiya Zakzaky ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka kan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara.

Cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Ibrahim Musa ya aika wa BBC ranar Lahadi ta ce ta yi imanin gwamnan ya ɗauki matakin ne sakamakon matsin lamba daga abin da ta kira “wasu malamai da ba su jituwa da malamin.”

Ta ce matakin haramta masa karatu da wa’azi ya saɓa wa ƙundin tsarin mulki da kuma dokokin ƙasashen duniya na keta haƙƙin ɗan Adam.

Gwamnatin Kano dai ta ɗauki matakin ne bayan samun umurnin kotu na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar da kuma hana shi wa’azi.

Hakan ya ta so ne bayan zarginsa da yin kalaman da ka iya tunzura jama’a a cikin wa’azin da yake gabatarwa.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *