
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani December 3, 2020 15
Ministan cikin gida na Faransa ya ce gwamnatin ƙasar za ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri da ba a taɓa ganin irinsa ba kan masallatan da ake zargi na karfafa tsatsauran ra’ayin addinin Islama.
Mista Gerald Darmanin ya ce za a fara ne da masallatai 76 a cikin kwanaki masu zuwa, wataƙila ma a rufe wasunsu idan ta kama.
Wannan dai shi ne sabon matakin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta dauka bayan hare-haren da ke da alaƙa da na masu tsatsauran ra’ayi a kasar.
A kwanakin baya ne aka fille kan malamin da ya nuna wa ‘yan ajinsa zanen Annabi Muhammad, wanda ake kallo a matsayin izgilanci ga addinin Islama da mabiyansa.
Zane-zanen da wasu Faransawa ke yi tare da alaƙantasu da wani addini na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a duniya, har ta kai ga ƙasashen Musulmai ƙauracewa kayan da Faransan ke samarwa.
A kwanan baya ne shugaba Emmanuel Macron ya nemi shugabannin Musulmai da su amince da abin da ya kira “tsarin mulkin Jamhuriyya” a wani ɓangare na yaƙar masu tsaurin kishin addinin Islama.
Dokar ta bayyana cewa Musulunci addini ne ba wata manufar siyasa ba, tare da haramta “katsalandan daga ƙasashen waje” a ƙungiyoyin Musulmi.
Mista Macron ya kuma kare tsarin manufofin Faransa bayan hare-haren da aka kai da suka ƙunshi har da fille kan malamin da ya nuna wa ɗalibai zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad a aji a watan jiya.
“Wasu sharuɗɗa za a rubuta su cikin launin baƙi da fari (cikin kundin): wato ƙin amincewa da manufar siyasa a addinin Musulunci da kuma duk wani katsalandan daga wata ƙasa,” kamar yadda wata majiya ta shaida wa jaridar Le Parisien bayan ganawar.
Wakilan majalisar Musulman ta CFCM sun kuma amince da kirkirar Majalisar Limamai ta Kasa, wadda za ta tantance malaman da ba su shaida a hukumance, wanda kuma za a iya janyewa idan an saɓa sharuɗɗan
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)