
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce an kashe Auwalu Daudawa, kasurgumin dan fashin dajin nan da ke da hannu wajen sace daliban sakandaren Kankara.
Kwamishinan Tsaron jihar, Abubakar Muhammad Dauran, ya shaida wa BBC cewa an kashe Daudawa ne sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da kungiyoyin ‘yan fashi da ke hamayya da shi.
A cewarsa, an kashe dan fashin ne tare da wasu mabiyansa lokacin da ya je satar shanu.
“A daren da ya gabata ne [Juma’a] muka samu labarin cewa an kashe Auwalun Daudawa… har ya dauki shanun wasu, kuma su ma wadannan ‘yan fashi da ke yankin sun dauki alkawarin ajiye makamansu. To, a wannan ne hadari ya same shi aka kashe shi. Labarin da yake zuwo mana ke nan,” in ji Kwamishina Dauran.
Ya kara da cewa har yanzu ba su kai ga tabbatar da wadanda suka kashe dan fashin dajin ba, “sai dai muna yin bincike a kan lamarin.”
Abubakar Dauran ya ce kodayake har yanzu ba su san inda gawar dan fashin dajin take ba, “amma ka san abu ne da ya kamata a yi bincike a gano ainihin takamaiman abin. Amma an tabbatar ga labarin da ke zowa lallai an kashe shi din.”
Ya ce akwai wadanda suka ga gawar dan fashin kuma ba shi kadai aka kashe ba, kodayake shi ma ya kashe wasu.
Kwamishinan ya ce Auwalun Daudawa ya je jihar ta Zamfara ne domin halartar daurin auren kannensa “don haka ya tafi da iyalinsa a kan cewa idan aka gama hidimar auren zai dawo, sai kuma ga shi a daren jiya wannan labari ya zo cewa wannan batu ya rutsa da shi.”
Abubakar Dauran ya ce suna jiran jami’an tsaro domin su yi musu karin bayani kan kisa kasurgumin dan fashin dajin, yana mai cewa ba su samu wannan bayani ba ne “domin lamarin ya faru ne da tsakar dare.”
A baya dai, Auwalu Daudawa ya ce ya tuba daga sana’ar fashin daji da kuma garkuwa da mutane har ma ya mika makamansa ga hukumomi, abin da ya sa gwamnatin Zamfara ta yi masa afuwa.
Sai dai rahotannin da suka nuna cewa ya je satar shanu ne aka kashe shi za su janyo muhawara kan dacewa ko akasin haka na yi wa ‘yan fashin daji afuwa.
A wata hira da kakafen watsa labaran Najeriya kwanakin bay, Auwalun Daudawa ya bayyana cewa shi ne ya shugabanci barayin dajin da suka sace ‘yan makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina su fiye da 300 a watan Disambar 2020.
Satar daliban maza ta jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, kodayake daga bisani gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya shaida wa BBC cewa kungiyar Fulani ya Miyetti Allah ce ta jagoranci yin sulhu domin kubutar da su.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)