play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Duniya
  • keyboard_arrow_right Zanga-zanga ta ɓarke a Iraki bayan gobarar da ta hallaka mutum 60 a asibiti

Labarai

Zanga-zanga ta ɓarke a Iraki bayan gobarar da ta hallaka mutum 60 a asibiti

Bello Sani July 13, 2021


Background
share close

ye da mutum 60 ne suka mutu bayan da gobara ta tashi a sashen da aka keɓe don jinyar masu cutar korona a wani asibiti a birnin Nasiriya na ƙasar iraƙi.h

Mafi yawan asibitoci a Iraƙi na cikin yanayi marar kyau bayan shafe shekaru ana rikici, sannan dangin mutanen da suka rasa rayukan nasu sun taru a wajen asibitin suna nuna ɓacin rai.

Ba a gano abin da ya jawo tashin gobarar ba, amma rahotanni sun ce ta faru ne bayan da tulun iskar oxygen ya yi bindiga.

Firaministan Iraƙi Mustafa al-Kadhimi ya bayar da izinin kama shugaban asibitin.

Kafar yada labaran ƙasar ta ce mutum 64 ne suka mutu, sannan kusan 70 suka jikkata.

Shugaban majalisar wakilan Iraƙi, Mohammed al-Halbousi, ya wallafa a Tuwita cewa gobarar “alama ce ƙarara da ke nuna gazawa wajen kare rayukan ƴan Iraƙi, kuma dole a kawo ƙarshen wannan masifa da ta faru”.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an yi artabu tsakanin mutane da ƴan sanda a wajen, har ma an cinna wa motocin ƴan sanda biyu wuta.

Sabon sashen marasa lafiyar yana da gadajen kwanciya 70 kuma bai wata uku da gina shi ba, kamar yadda jami’an lafiyar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Wani ma’aikacin lafiyaya ce a ƙalla mutum 63 na cikin sashen a lokacin da wutar ta tashi.

“Na ji wata ƙara a cikin sashen da aka killace masu cutar korona kuma nan da nan sai gobara ta tashi,” in ji wani maigadin asibitin da ya yi hira da Reuters. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.

A watan Afrilu, fashewar wani tulun iskar oxygen ya jawo gobarra da ta hallaka a ƙalla mutum 82 tare da jikkata 110 a wani asibiti a babban birnin ƙasar Baghdad. Ministan Lafiya Hassan al-Tamimi ya yi murabus bayan faruwar lamarin.

Annobar cutar korona ta yi matuƙar tagayyara fannin lafiyar Iraƙi, wanda dama yake cikin ha’ula’i sakamakon yaƙin da aka shafe shekaru ana yi da kuma cin hanci da ya yi wa ƙasar katutu.

Mutum miliyan 1.4 ne suka kamu da cutar korona a Iraƙi, saannan 17,000 sun rasu, a cewar jawaban Jami’ar Johns Hopkins.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *