play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Zaben 2023: ‘Tsarin karɓa-karɓa ba zai yi tasiri tsakanin APC da PDP ba’

Siyasa

Zaben 2023: ‘Tsarin karɓa-karɓa ba zai yi tasiri tsakanin APC da PDP ba’

Bello Sani July 3, 2021 20


Background
share close

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da tsarin karɓa-karɓa zai fidda ita a zaɓen shekara ta 2023 – batun da ke ci gaba da ɗaukan hankalin jama’a da ma ƴan siyasar ƙasar.

Har yanzu dai jam`iyyar APC mai mulki ba ta bayyana shiyyar da za ta bai wa takarar shugabancin kasar ba.

Alhaji Isa Tafida Mafindi wanda jigo ne a APC ya shaida wa BBC cewa wajibi ne jam`iyya ta ba da fifiko ga cancanta, idan tana so ta kai bantenta a shekarar 2023.

Da yake tsokaci kan batun miƙa mulkiKudancin Najeriya kuwa, Mafindi ya bayyana cewa “zamanin Jonathan Arewa ta yi wa Kudu kara, Arewa ta danne zuciya, da aka ce a haɗu a yi, ai raba ƙafa suka yi Kudu maso Yamma,

inda Buhari bai samo ƙuri’u da ya samu daga Borno da Kano da Katsina da Kaduna da sauransu ba. da tuni sun hade da abokanansu suna mana gwalo”. in ji shi.

Mafindi ya ce a ra’ayinsa, yana ganin mutumin da ya fi dacewa ya shugabanci ƙasar shi ne ɗan Najeriya da bai kai shekara 60 ba da haihuwa.

“A dubi wa zai sarrafa mana nama ya fidda ita da manta daga wuta, muna da irin waɗan nan haziƙan samari suna ko ina”. in ji jigon.

Ya ƙara da cewa ba ya goyon bayan shiyya saboda a ganinsa biyan buƙatun ƴan Najeriya kuma ya kasance an sa Najeriya a gaba shi ne abu na farko da ya kamata a fi mai da hankali a kai.

Masharhanta dai na yi wa al’amarin karba-karba kallon wani abu da ‘yan kasar suka kirkira ba don yana cikin tsarin mulkin kasar ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *