play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yawan sace-sacen dalibai na kassara harkar ilimi a arewacin Najeriya – Masana

Labarai

Yawan sace-sacen dalibai na kassara harkar ilimi a arewacin Najeriya – Masana

Bello Sani July 6, 2021 12


Background
share close

Masana a Najeriya sun bayyana fargaba kan makomar ilimi a ƙasar ganin yadda batun sace-sacen dalibai ke kara ta’azzara musamman a arewacin kasar.

O

Masanan na ganin matuƙar mahukunta ba su gaggauta shawo kan lamarin ba, zai iya haddasa gagarumar koma-baya wajen ci gaban ilimi a yankin.

Masu sharhi a kan al`amuran yau da kullum, irin su Mallam Isa Tijjani ya fada wa BBC cewa irin wadan nan hare-haren na kassara harkar ilimi a arewacin Najeriya.

  • Yadda aka sace mutum 22 har da jarirai a Kaduna
  • Yadda mutanen Zaria suka yi wa ƴan bindiga Sallar Al-qunut da addu’oi
  • Rashin tsaro: Manyan dazukan da ƴan ta’adda ke samun mafaka a arewacin Najeriya

“Kame yan makaranta da ake yi a debe su daga makarantunsu, yana da mummunan tasiri a kan koma-bayan ilimi a Arewacin Najeriya musamman ilimin ƴaƴa mata,

“Daman iyayenmu ba karfi suke bayarwa game da zancen ilimin nan ba kuma a zo ana yi wa yara yan kanana irin wannan wulakanci, ta ya ya iyayenmu za su samu karfin zuciyar barin yaransu su ci gaba da makaranta?”, in ji Mallam Isa Tijjani.

Ya kara da cewa irin wannan matsala a yanzu ta sa iyaye ma na janye yayansu maza daga makaranta.

Shi ma masanin harkar tsaro, Dr Kabilru Adamu na kamfanin Beacon Consulting, ya ce za a iya dakile `yan bindigar idan gwamnatoci suka hada kai suka kuma samu hadin kan al`umma.

Ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su hada kai domin magance yan fashin dajin da suka mamaye dazuzzuka.

Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta magance matsalar kwararar makamai a cikin kasar.

“Gwamnati ta fito da wata sabuwar ma’aikata, ya kamata mu ga ma’aikatar nan ta fara aiki”. in ji masanan tsaron.

Bayanai sun nuna cewa akwai mimanin dalibai dubu daya da yan bindiga suka sace tun daga watan Disamban bara zuwa wannan lokaci kuma fiye da 300 har yanzu na hannunsu.

A watan Disamban bara ne `yan bindiga suka sace `yan makarantar sakandaren Kankara da ke jihar Katsina su fiye da 340.

Ba a yi nisa ba a cikin watan Fabrairun wannan shekarar, sai `yan bindigan suka sake sace daliban sakandaren mata ta Jangebe da ke jihar Zamfara su fiye da 300 kuma a wannan watan ne suka sace daliban sakandaren Kagara 27.

Sai watan Maris na wannan shekarar da aka sace dalibai 37 a makarantar nazarin gandun daji ta Afaka da ke jihar Kaduna.

Shi ma watan Afirilu na kunshe da labari marar dadi na sace daliban Jami`ar Greenfield da ke jihar Kaduna.

Sai watan Mayun wannan shekarar, inda nan ma aka sace daliban Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Niger su fiye da dari, ciki har da kananan yara `yan shekara uku da haihuwa.

Kazalika, a watan Yunin da ya wuce ma an sace daliban kwalejin gwamnatin tarayya da ke Yauri a jihar Kebbi, inda har zuwa yanzu mahukunta ba su fadi aihinin adadinsu ba.

Sai kuma a baya-bayan nan, satar daliban sakandaren Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna wadanda su ma mahukunta ba su fadi yawansu ba, amma wasu shaidu sun ce akalla sun kai 130.

Mahukunta a Najeriya dai na ikirarin cewa suna daukar matakai da nufin murkushe `yan bindiga, tare da samar da kariya ga dalibai.

Sai dai, ganin cewa kimanin dalibai dari uku na hannun `yan bindigan, zai yi wuya iyayen wadannan yara su saurari maganar gwamnati, sai sun ga komawar `ya`yansu gida cikin koshin lafiya.

Kazalika akwai jan aiki na sake gamsar da su, da sauran masu `ya`ya cewa `ya`yan nasu ba za su sake fadawa hannun barayi ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *