play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Yanzun nan: Tashin hankali yayin da majalisa ta yi watsi da dokar zabe ta Buhari

Labarai

Yanzun nan: Tashin hankali yayin da majalisa ta yi watsi da dokar zabe ta Buhari

Bashir Sani March 9, 2022 46


Background
share close
  • Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudurin dokar zabe da shugaba Buhari ya gabatar saboda wasu dalilai
  • A baya majalisar ta fusata da jin yadda kotu ta ba da umarni gareta cewa, kada ta sake ta gyara dokar zaben
  • A yau dai majalisar ta kawo karshen magana, ta kada kuri’a kuma an yi watsi da dokar gabanin karatu na biyu

FCT, Abuja – Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, majalisar dattawa a ranar Laraba ta yi watsi da kudirin doka da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na neman gyara dokar zabe ta 2022.

Kudirin doka mai taken: “Kudirin dokar da zai gyara dokar zabe ta 2022 da kuma abubuwa masu alaka, 2022,” Sanatoci sun yi watsi da shi, lamarin da ya dakatar da karatun kudurin na biyu.

Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko a ranar Talata duk da umarnin da kotu ta bayar na hana Majalisar Dattawa yin aiki akansa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kalubalanci hukuncin kotun yana mai cewa a kowane hali, bangaren shari’a bai da ikon hana majalisar gudanar da ayyukanta na tsarin mulki.

Kafin Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin a ranar Laraba, Sanata Adamu Aliero, yayin da yake karanto doka ta 52 (5) na Majalisar Dattawa, ya bukaci Shugaban Majalisar da ya yi watsi da shawarar duba ga kudirin.

Sai dai Lawan ya dage. Ya sake jaddada matsayinsa na cewa Sanatoci ne ke da hakkin kin amincewa da kudirin ba bangaren shari’a da ke neman hana majalisar gudanar da ayyukanta ba

Saboda haka, Sanatoci sun kada kuri’ar kin amincewa da kudirin na hana sake karanta shi a karo na biyu. Karin bayani na nan tafe…

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *