play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yan bindiga sun kashe mutum 66 a Karamar Hukuma daya a jihar Kebbi

Labarai

Yan bindiga sun kashe mutum 66 a Karamar Hukuma daya a jihar Kebbi

Bello Sani June 5, 2021 57


Background
share close

Rundunar ‘yansada Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 66 a karamar hukumar Danko-Wasagu tare da cewa ana fargabar adadin zai iya wuce haka.

Kakakin rundunar ‘yansanda na Jihar DSP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana wa BBC hakan yana cewa harin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 3 na rana, a kauyuka takwas na karamar hukumar.

A cewar kakakin kauyukan sun hada da Kimpi da koro da Dimi da Zutu da Rafin Gora da Iguenge.

Yace harin ya fi shafar manyan maza sai kuma mata, amma har yanzu ba su kai ga tantance adadin matan da abin ya rutsa da su ba.

Ko a watan jiya sai da ‘yan bindiga suka farwa karamar hukumar suka kashe ‘yan sanda tara cikin har da DOP yankin.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *