Kasar Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich, kana ta sanya haramcin mu’amala da daidaikun mutane da ‘yan kasuwa na Burtaniya, da dokar hana zirga-zirga duk dai akansa.
Sky Sports ta rahoto Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson yana cewa:
“Ba zai yiwu a samar da mafaka ga wadanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ya kai wa Ukraine ba.”
Wani daftarin gidan gwamnati da aka fitar a ranar Alhamis ya ce Abramovich yana da “dangantaka ta kud da kud ta tsawon shekaru” da shugaban Rasha, Vladimir Putin, inji rahoton The Athletic.
Hakazalika, ya kara da cewa:
“Takunkumin na yau shine mataki na baya-bayan nan na goyon bayan da Birtaniya ke baiwa al’ummar Ukraine ba tare da kakkautawa ba.
“Ba za mu sassauta ba wajen kuntatawa wadanda suka taimaka wajen kashe fararen hula, lalata asibitoci da kuma mamaye wasu ‘yan uwa ba bisa ka’ida ba.
Har ila yau, sakatariyar harkokin wajen Burtaniya Liz Truss ta ce:
“Takunkumin na yau ya sake nuna cewa ‘yan kama karya da masu cika aljihu da kudin kasa ba su da wani matsayi a cikin tattalin arzikinmu ko kuma al’ummarmu. Kusancinsu da Putin ke nuna suna da hannu wajen ta’addancin nasa.
“Jinin al’ummar Ukraine na hannunsu, ya kamata su rataye kawunansu saboda kunya.
“Goyon bayanmu ga Ukraine ba zai kassara ba.
Ba za mu tsaya wata-wata ba a wannan aiki na kara matsi kan gwamnatin Putin da kuma kassara kudaden na’urar yakinsa na zalunci ba.”
Post comments (0)