
El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ta yuwu mace ce zata maye gurbinsa idan lokacin saukar sa ya yi a 2023 Ya yi wannan bayani ne a ranar Talata […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Plateau – Daily Trust ta rahoto cewa tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya wato Super Eagles, Justice Christopher, ya mutu.
A cewar majiyoyi, tsohon dan wasan tsakiyan ya fadi ne a otal din sa dake Gwolshe, wajen Tudunwada Ring road, Jos da sanyin safiyar Laraba, 9 ga watan Maris.
Daily Trust ta tattaro daga makusantan tsohon dan wasan cewa yana ta fama da cutar hawan jini wanda bai yi tsanani ba.
Gani na karshe da aka yiwa marigayin ya kasance a ranar Talata a cikin abokansa cike da koshin lafiya kuma babu wata alama da ke nuna matsananciyar rashin lafiya a tare da shi.
Koda dai rundunar yan sandan Filato bata riga ta tabbatar da mutuwar Tasa ba, an rahoto cewa an kai gawarsa ajiya a asibitin kwararru na Filato.
Wata majiya ta ce ana sanya ran za a yi gwaji don gano abun da ya kashe shi a asibitin kafin a binne shi.
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ta yuwu mace ce zata maye gurbinsa idan lokacin saukar sa ya yi a 2023 Ya yi wannan bayani ne a ranar Talata […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)