Kotu ta tsayar da ranar shari’ar Zakzaky
A ranar Laraba da ta gabata wata babbar kotun jiha a Kadunan Najeriya ta tsayar da ranar yanke wa Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa Malama Zinat hukunci.
Kotun ta tsayar da ranar 28 ga wannan watan na Yuli domin yanke wa jagoran ƙungiyar ƴan shi’a ta IMN
Gwamnatin jihar Kaduna ce ta gurfanar da su a gaban kotun kan tuhume-tuhume da dama ciki har da aikata kisan kai da gangan da gudanar da taro ba bisa ƙa’ida ba.
Lauyoyin Sheikh Ibrahim Zakzaky bisa jagorancin Femi Falana, sun gabatar wa da kotun buƙatar ta yi watsi da ƙarar saboda a cewarsu an gaza tabbatar da tuhume-tuhumen, ko da yake lauyoyin da suke ƙara sun buƙaci kotun ta ci gaba da shari’ar la’akari da shaidun da suka gabatar.
Post comments (0)