play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

Labarai

Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

Bello Sani June 28, 2021 14


Background
share close

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan karuwar aikata laifuka a kasar yana mai cewa galibinsu shan miyagun kwayoyi ne ke jawo su.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tir da bayyanar kungiyoyin asiri a makarantun sakandare da firamare

A cewarsa, wannan ba karamin abin takaici bane saboda ya kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Jonathan yace:

“Yanzu muna da kungiyoyin asiri a makarantun firamare da sakandare, a baya ya tsaya a manyan makarantu, amma yanzu zaku ga yara a wadannan makarantun suna tunanin yadda za su kashe sa’anninsu, wannan abin bakin ciki ne.”

Da yake halartar taro ta yanar gizo a ranar Juma’a, Jonathan ya kara da cewa matsalolin tabin hankali sun zama kalubale kasancewar mafi yawan ‘yan Najeriya suna cikin halin damuwa da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.

Mafi yawan wadannan laifuffukan da aka tabbatar, shan kwayoyi ne suka haifar da su, saboda babu wani dan Najeriya mai hankali da zai je ya aikata laifi sai dai idan yana cikin mayen wani abu.

Ka yi tunanin farkawa da labarin kisan kai da safe, zai bar ka da tunani a zuciyar ka. Har ila yau, ya kamata mu kuma bincika batun lafiyar kwakwalwa.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi ya haifar da manyan hadurra ga Najeriya fiye da ayyukan ‘yan ta’adda mabambanta.

Shugaban na Najeriya ya yi wannan bayani ne a ranar 26 ga Yuni, a yayin kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi na WADA, The Nation ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da dole ne a yi shi ba kakkautawa.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *