Kebbi – Yan bindiga sun sake kashe jami’an tsaro 19 cikinsu akwai sojoji 13, a jihar Kebbi, a cewar wata majiyar tsaro da mazauna gari a ranar Laraba, rahoton The Punch.
An yi artabun ne a daren ranar Talata a kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, kwana guda bayan an kashe dimbin yan sakai a yankin.
Daruruwan yan bindiga sun afka Kanya, inda suka fafata da sojoji da yan sanda na tsawon awa uku a cewar majiya da kuma mazauna garin.
“Yanzu mutane 19 aka tabbatar da mutuwarsu. Sun hada da sojoji 13, yan sanda biyar da dan vigilante daya, ” a cewar majiyar tsaro da baya so a ambaci sunansa, ya shaida wa AFP. Saurari karin bayani…
Post comments (0)