play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Yan sanda sun bayyana daliin da yasa Fulani suka kashe mutum 7 a jihar Taraba

Tsaro

Yan sanda sun bayyana daliin da yasa Fulani suka kashe mutum 7 a jihar Taraba

Bashir Sani March 8, 2022 28


Background
share close
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar mutum 7 a wani harin ɗaukar fansa da Fulani makiyaya suka kai
  • Kakakin yan sanda, Abdullahi Usman, yace lamarin ya fara ne tun lokacin da aka harbi wani makiyayi a kafa yana tsaka da kiwo a Tor Damisa
  • Lamarin da ya fusta Fulanin suka yi yunkurin ɗaukar fansa, kafin jami’an tsaro sƴ dakatar da su, suka kashe mutane

Taraba – Mutum 7 cikinsu har da mace aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka farmaki ƙauyen Tor Damisa, ƙaramar hukumar Donga, jihar Taraba.

Harin wandaa ake tsammanin na ɗaukar fansa ne ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu mayaƙan Tiv sun ji wa makiyayi munanan raunaka yayin da yake kiwon dabbobinsa a yankin kauyen.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels tv, ya ce maharan sun kona gidaje.

A cewarsa, Dakarun soji, yan sanda na yan Bijilanti sun baza komar su ko ina da nufin cafke makasan da kuma gurfanar da su doka ta yi aikinta.

Hukumar yan sanda ta bayyana yadda abun ya faru tun farko, Kakakin yan sandan ya ce:

“An ceci wani matashin ɗan Fulani a jeji, ya sha harbin bindiga a ƙafa, ya karye a wurare da yawa a jikinsa, aka kawo shi gaban DPO a can garin Donga. Da aka tambaye shi abin da ya faru, yace mayakan Tiv ne suka harbe shi.

Bayan gano ɗan jihar Filato ne, aka tuntubi yan uwansa kuma aka damƙa musu shi domin cigaba da kula da lafiyarsa a Asibitin koyarwa na Filato.”

“Bayan tafiya da shi, Fulanin dake zaune a kauyen Tur Damisa bisa zargin yan ƙabilar Tiv suka shirya suka kai musu hari.”

Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

Usman ya ƙara da cewa bayan sammun rahoto, jami’an soji, yan sanda da mafarauta suka nufi yankunan, amma bisa rashin sa’a kafin isar su Fulanin sun kaddamar da harin.

“Kafin isar jami’an tsaro tuni Fulanin sun kai harin yankin yan ƙabilar Tiv, suka buɗe musu wuta kan mai uwa da wabi, mutum 7 suka mutu.” “Yayin da Dakaru suka isa sun kwantar da hankulan mutane, komai ya dawo dai-dai, yanzu haka sun bazama neman maharan. Yanzu haka komai ya dawo dai-dai.”

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *