- Kachalla Bello Turji Birnin Fakai ya karyata zargin cewa miyagun ‘yan bindiga ba cikakkun musulmai ba ne
- Gawurtaccen ‘dan bindigan ya yi martani a kan wata magana da Shehin malami Bello Yabo ya taba yi a baya
- Bello Turji ya ce Sheikh Bello Yabo ya yi masa karya, kuma Allah zai saka masa domin ba ya wasa da sallah
Zamfara – Bello Turji ya yi magana a game da zargin da babban malamin musulunci, Bello Yabo ya yi masu, inda ta kai ya zargi musuluncin ‘yan bindiga.
Bello Turji ya musanya wannan zargi a wata hira da Aminiya ta yi dashi. Gawurtaccen ‘dan bindigan ya ce shi cikakken musulmi ne.
Turji ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Aminiya, an ji Turji yana janyo wata aya daga cikin Suratul Ali Imran a cikin Al-Kur’ani domin ya kare kan sa.
Ayar da Bello Turji ya jawo tana cewa Musulunci ne kadai addinin gaskiya a wajen Allah (SWT).
Musulunci ne addini – Turji
Shararren ‘dan ta’addan da ya addabi kasar Sokoto da Zamfara ya ce duk wani malamin da ke Duniya ya san da wannan aya da kuma abin da ta ke nufi.
Kachalla Turji Birnin Fakai wanda ya fi shahara a ko ina da Bello Turji ya ce malamin adddinin musuluncin ya yi masa karya, kuma Ubangiji zai saka masa.
Domin tabbatar da cewa bai bar musulunci ba, Turji ya kafa hujja da cewa yana yin sallah, dalili kuwa yana jin tsoron haduwarsa da Allah Madaukakin Sarki.
“Sannan kuma ya yi magana cewa ba mu bin addini, ai addini ba na shi ba ne, na Allah da ya halicce mu ne. Ko mun yi ba zai gane ba.”
“Saboda ina gudun haduwa ta da shi (Allah).” – Bello Turji
Ba a taba kai ni kurkuku ba
Bugu da kari, Tuji ya ce bai taba zuwa gidan yari ba, akasin shehin malamin da yake zarginsa.
“Idan ma Malami ne na gaskiya, ko bai taba yi wa kowa karya ba, to ni ya yi mani karya. Saboda haka, sai Allah SWT ya isar mani.”
“Ni ban taba zuwa kurkuku ba, duk jami’in tsaron Najeriya bai taba kai ni ko dakin ‘yan sanda ba, balle Yabo ya ce ya gan ni a kurkuku.”
“Karya yake yi tsagwaronta. Kuma ya bude baki ya ce Turji barawo ne, ba ya sallah, da sauransu, wannan ra’ayinsa ne kurum ya fadi.”
“Sannan shi Turji ya san abin da yake yi, Allah da yake bautawa ya sani, don haka ba sai ya zo, ya fadawa Bello bukatar da yake ciki ba.”
Hukuncin musuluncin Turji
Legit.ng Hausa ta tuntubi wani malamin musulunci a garin Zaria, Yusuf Muhammad Ladan domin jin ta sa.
Ustaz Yusuf Muhammad Ladan ya bayyana cewa kisan kai yana cikin mafi girman zunubi a Musulunci, kuma Allah ya yi wasu alkawura biyar ga mai kashe jama’a.
Malamin ya fada mana cewa a halin yanzu, ba za a fitar da Turji daga musulunci ba, amma musulmi ne shi mai babban laifi, duk da haka yana da damar ya tuba.
Tarkon da aka yi wa duk mai kashe Bayin Allah shi ne zai shiga wutar jahannama, kuma zai dawwama a cikinta, sannan zai gamu da fushin Allah da tsinuwarSa.
Post comments (0)