play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000 inji gwamnatin jihar Zamfara

Tsaro

Tubabbun yan bindiga sun ajiye makamai sama da 1000 inji gwamnatin jihar Zamfara

Bello Sani May 27, 2021


Background
share close

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tubabbun yan bindigan da suka addabi jihar a baya kawo yanzi sun ajiye makamai sama da dubu guda karkashin shirin sulhun da gwamnatin ta yi.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Garba Dauran, ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, birnin jihar.

Dauran ya ce lissafa jerin kananan da manyan makamai da albursai da yan bindigan suka ajiye.

A cewarsa, wadannan makamai sun hada da:

1. Bindigogin gargajiya 887

2. Manyan makami 203

3. Albursai 2,566

4. Akwatin lodin albursai na AK-47 guda 64

5. Ankwa 2

A riwayar Daily Nigerian, kwamishanan ya yi kira da shugabannin gargajiya su taimaka wajen lura da yankunansu don gano yan bindiga.

A ranar 7 ga Febrairu, gwamnatin jihar Zamfara ta shiga sulhu da yan bindigan da suka addabi jihar domin neman saukin hare-hare.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *