play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai wa Matimakin Gwamna hari a kan hanya

Tsaro

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai wa Matimakin Gwamna hari a kan hanya

Bashir Sani March 9, 2022 22


Background
share close

Kebbi – Tsagerun yan bindiga sun farmaki jerin gwanon motocin mataimakin gwamna jihar Kebbi, Samaila Yombe, ranar Talata da daddare.

Vanguard ta tattaro cewa yan ta’addan kai wa tawgaar mataimakin gwamnan hari ne tsakiyar kauyen Kanya da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

A cewar sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Abdullahi Yalmo, waɓda ya tabbatr da faruwar lamarin, ya ce jami’in ɗan sanda ASP Idris Umar Libata, ya rasa rayuwarsa.

Ya ce ɗan sandan ya rasa rayuwarsa ne yayin d asuka tarbi yan bindigan, suka yi musayar wuta tsakanin su.

Daga ina mataimakin gwamnan ya fito?

Yalmo ya yi bayanin cewa uban gidanasa tare da rakiyar kwamandan barikin sojojin Najeriya dake Zuru domin zuwa ta’aziyya da jaje ga iyalan mutanen kauyen Kanya.

Mataimakin gwamnan yaje ta’aziyya ne biyo bayan wani mummunan lamarin da ya faru da harin yna bindiga, wanda ya lakume rayukan aƙalla yan Bijilanti 68, da kuma wasu fararen hula da dama.

Sakataren watsa labaran mataimamin gwamnan yace:

“Allah ya tseratar da Uban gidan mu, amma bisa rashin sa’a ya yi rashin ɗaya daga ciki haziƙan yan sandan dake tare da shi.”

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihr Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai ɗaga kiran wayar da aka jera masa ba domin tabbatar da abin da ya auku.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *