play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tattalin Arziki
  • keyboard_arrow_right Tsadar kayan abinci: ‘Ƴan Najeriya za su ci gaba da ɗanɗana tsadar rayuwa’

Labarai

Tsadar kayan abinci: ‘Ƴan Najeriya za su ci gaba da ɗanɗana tsadar rayuwa’

Bello Sani August 16, 2021 16


Background
share close

Masana tattalin arziki a Najeriya na gargaɗin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi, cewa hauhawar farashin kaya da ake fama da ita a kasar za ta sauka.

Shi dai bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022 farashin kayan abinci zai sauka da kashi goma cikin dari, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.

Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra’ayi, kuma ya shaida wa BBC cewa matsawar mahukunta ba su tashi tsaye wajen daukar matakin da ya kamata ba, lamarin zai ci gaba da dagulewa ne maimakon ya gyaru.

“Abu ne mai wuya a iya samun wani cigaba, saboda halin da muka samu kanmu, ga rashin aikin yi, ga matsalar tsaro an kasa magance ta, don haka dukkan wadannan matsaloli akwaisu, kuma baza su bada damar haifar da wani sauyi ba” in ji masanin.

Ya ƙara da cewa “abun da gwamnati ya kamata ta yi shi ne ta fadada hanyoyin samun kudi, domin ta iya aiwatar da manufofinta na yau da kullum, sannan a samar da zaman lafiya don in akwai shi to mutane za su iya fita su nemi na kansu”.

A baya bayan nan ne Bankin Duniya ya ba da rahoton cewa sama da mutum miliyan bakwai sun sake faɗawa talauci a bara kawai saboda ƙaruwar hauhawar farashi a Najeriya.

Bankin ya ce a cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.

Rahoton na Bankin Duniyar ya yi nuni da abin da ya kira da fitattun garanbawul na gwamnati, da nufin shawon kan tasirin anobar cutar korona da kuma tallafawa wajen farfado da tattalin arziki, cikin su har da matakan rage tallafin man fetur, da daidata farashin wutar lantarki.

Dukkansu kuma in ji rahoton don bunkasa kafofin samun kudin shiga da nufin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar talaka ne

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *