play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Sunday Igboho: Yadda DSS ta gano manyan bindigogi da alburusai a gidan jagoran ‘yan a-waren Yarabawa

Labarai

Sunday Igboho: Yadda DSS ta gano manyan bindigogi da alburusai a gidan jagoran ‘yan a-waren Yarabawa

Bello Sani July 2, 2021 25


Background
share close

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta ce ta gano manyan bindigogi da alburusai a gidan mai rajin kare Yarabawan nan Sunday Igboho.no8

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta ce jami’anta ne suka kai sumame gidan Sunday Adeniyi Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ke Soka, a Ibadan da ke jihar Oyo.

Hukumar ta ce ta tura jami’an nata ne sakamakon samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya tara makamai a gidan.

Sanarwar, mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Peter Afunanya, ta ce lokacin da jami’an suka isa sai wasu mutane tara da take zargin masu gadin Igboho ne suka far musu dauke da bindigogi kirar AK-47 da kuma wasu uku da bindigogi kirar harbi-ka-ruga.

“A yayin musayar wutar an bindige mutane biyu da aka tarar a gidan Igboho dauke da makamai yayin da kuma aka kama sauran”, a cewar DSS.

DSS ta ce jami’inta daya ne kacal maharan suka harba a hannunsa na dama.

Hukumar tsaron farin kayan ta Najeriya ta ce ko a ranar Lahadi, Igboho da jama’arsa sun kitsa kai hari da sunan neman yancin kafa kasar Yarbawa, don haka a cewarta “Wannan kame da ta yi tabbaci ne na wani babban shiri da mutumin da yaransa ke yi na tada zaune tsaye a Najeriya”.

Don haka ne take jan hankalin kasashen duniya bisa tunanin watakila zai iya neman sabunta takardun shaidarsa na zama a wata kasa bisa basu hujjar cewa sun bace.

DSS ta ce Sunday Igboho ya tsallake ya fice daga cikin gidan lokacinda jami’anta ke gwabzawa da yaransa.

Kazalika ta umarce shi da ya mika kansa don fuskantar bincike a kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *