play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC

Siyasa

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Ƙwace Kujerar Gwamna Da Mataimakinsa Saboda Sauya Sheƙa Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC

Bashir Sani March 8, 2022 53


Background
share close
  • Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe sun rasa kujerunsu saboda ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC
  • Kotun ta yanke hukuncin cewa kuri’un da suka samu yayin zaben gwamna na jam’iyyar PDP ne don haka Umahi da mataimakinsa sun rasa kuri’un bayan ficewarsu daga jam’iyyar
  • Kotun ta umurci INEC ta karbi zabin sunayen wadanda za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP ko kuma ta sake sabon zaben gwamna a jihar

FCT, Abuja – Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, a kori Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, bayan sun fice daga jam’iyyar PDP sun koma APC mai mulkin sa, rahoton Vanguard.

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri’u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Mari na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam’iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

A cewar kotun, bayan komawa jam’iyyar APC, Umahi da mataimakinsa, ba PDP kadai suka bari ba, sun raba kansu da kuri’u jam’iyyar ta PDP, Daily Trust ta rahoto.

Kotun ta ce idan aka yi la’akari da sakamakon zaben na gwamna, kujerar gwamnan Jihar Ebonyi da mataimakinsa, ‘mallakar wanda suka yi karar ne ba wata jam’iyyar daban ba.’

“Babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin kasa da ya nuna ana iya musayar kuri’u daga jam’iyya daya zuwa wata jam’iyyar.”

Ta ce jam’iyyar PDP ce ke da kuri’un da kujerun da masu zabe a Jihar Ebonyi suka kada, don haka ba za a iya mika wa Gwamna Umahi da mataimkinsa kuri’un ba idan sun fice daga jam’iyyar.

Don haka kotun ta bada umurnin cewa nan take Dave Umahi da Igwe su ajiye mukamansu.

Kotu ta umurci INEC ta karbi sunayen wadanda za su maye Umahi da mataimakins daga PDP ko ta sake sabon zabe

Ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta karbi sunayen mutanen za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP, ko kuma ta sake yin sabon zabe a jihar Ebonyi kamar yadda sashi na 177(c) na kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima ya ce.

Kotun ta kuma hana Umahi da mataimakinsa Igwe cigaba da amsa sunan gwamna da mataimakinsa na jihar Ebonyi.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da jam’iyyar PDP ta shigar bayan Umahi da mataimakinsa sun koma APC. Saurari karin bayani……..

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *