play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Wata Sabuwa: Mambobin APC Sun Kawo Wargi, Sun Nemi A Dage Taron Gangamin 26 Ga Wata

Siyasa

Wata Sabuwa: Mambobin APC Sun Kawo Wargi, Sun Nemi A Dage Taron Gangamin 26 Ga Wata

Bashir Sani February 2, 2022 29


Background
share close
  • An bukaci jam’iyyar APC mai mulki da ta gaggauta dage shirinta na gudanar da taron gangamin jam’iyyar na kasa da aka shirya a watan nan
  • ‘Yan jam’iyyar mazauna kasar Birtaniya ne suka yi wannan kiran a ranar Talata 1 ga watan Fabrairu
  • Mambobin jam’iyyar APC a kasar Birtaniya sun ce kamata ya yi jam’iyyar ta mayar da hankali wajen ganin an warware rikicin da ke tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a matakai daban-daban

Landan, Burtaniya – A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ke shirin gudanar da taron gangaminta na kasa, reshen jam’iyyar na Burtaniya (UK) ta shawarci majalisar zartarwar jam’iyyar ta kasa da ta sake shawara.

Jam’iyyar APC reshen Burtaniya ta shawarci jam’iyyar da ta hada karfi da karfe kan cimma nasarorin da Gwamna Mai Mala Buni ke son cimmawa a kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC).

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC reshen Burtaniya, Philip Idaewor, wacce aka aikowa Legit.ng, kungiyar ta yi imanin cewa yana da kyau jam’iyyar ta samu karin dalilan sasanta ‘ya’yanta.

Idaevor ya ce ‘ya’yan jam’iyyar a kasar Birtaniya suna son hukumomin APC su sauya taron gagamin na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu zuwa wani lokaci daban.

Ya ce shawarar za ta tabbatar da samun halartar ‘ya’yan jam’iyyar dake kasashen waje domin ba za su iya ware kudaden jigila har sau biyu ba zuwa Najeriya don halartar taruka biyu.

Jam’iyyar APC reshen kasar Birtaniya ta yi kira ga hukumomin jam’iyyar da su yi kira ga jam’iyyar da ta dage taron domin moriyar dukkanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ya kara da cewa, samar da hadin kai, zaman lafiya da fahimta a cikin jam’iyyar ya fi komai dacewa fiye da taron gangamin da nan da makonni uku masu zuwa zai kara dagula jam’iyyar.

Idaewor ya ce rahotanni daga gida (Najeriya) game da yadda jam’iyyar APC ke fama da ‘yan tawaye da dama a yawancin jihohinta ba su da kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu lamuni a zabe mai zuwa na 2023.

A ci gaba da yin kira ga shugabannin jam’iyyar da su tashi tsaye wajen sasantawa, Idaevor ya ce jam’iyyar APC a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu nasarori da dama wajen gina kasar nan.

A wani labarin

saura kwanaki uku a yi taron gangamin APC, amma har yanzu jami’yyar bata sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ba game da taron da za a yi a ranar 26 ga Fabrairu, 2021 ba.

Kwamishinan wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’u na INEC, Mista Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Punch jiya Talata.

Okoye ya ce:

“Ba a sanar da hukumar ba game da wani taron gangami.”

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *