play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Sauya Sheƙa: PDP Ta Yunƙuro, Za Ta Maye Gurbin Matawalle Da Tsohon Mataimakinsa

Siyasa

Sauya Sheƙa: PDP Ta Yunƙuro, Za Ta Maye Gurbin Matawalle Da Tsohon Mataimakinsa

Bashir Sani March 10, 2022 56


Background
share close
  • Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara tana neman kotu ta maye gurbin Matawalle da tsohon mataimakinsa Mahdi Aliyu
  • Jam’iyyar ta PDP ta bakin lauyanta Emmanuel Ukala, SAN, ta ce tunda Gwamna Matawalle ya fice daga PDP ya koma APC, ya rasa kujerarsa
  • Lauyoyi masu kare Gwamna Matawalle da APC karkashin jagorancin Mike Ozekhome (SAN) su kuma sun nemi a basu lokaci domin su yi shiri

Zamfara – Babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar 17 ga watan Afrilu don sauraron karar neman tsige Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara saboda ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

A cikin karar, jam’iyyar PDP ta bukaci kotun ta ayyana tsigaggen mataimakin gwamna Mahdi Aliyu Gusau a matsayin hallastaccen gwamnan Jihar Zamfara.

PDPn ta kuma bukaci kotun ta kori yan majalisar tarayya da na jiha kimanin 37 da suka koma jam’iyyar APC, rahoton Daily Trust.

Mai shari’a Inyang Ekwo a ranar Alhamis ya tsayar da ranar sauraron shari’ar ne bayan lauyoyin da suka shigar sun bukaci a gwamutsa karrakin.

Lauyoyin wadanda aka yi kara, karkashin Mike Ozekhome (SAN) su kuma sun nemi a basu lokaci domin su shirya martaninsu kan karar.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *