play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su

Siyasa

Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su

Bashir Sani March 9, 2022 31


Background
share close
  • Majalisar dattawa ta tabbatar da sabbin kwamishinonin hukumar ICPC biyar bayan shugaban kasa Buhari ya zabe su
  • Majalisar ta tabbatar da kwamishinonin ne a zamanta na yau Laraba, 9 ga watan Maris
  • Hakan ya biyo bayan samun rahoton kwamitin majalisar wanda ya tantancesu karkashin jagorancin Sanata Suleiman Abdu Kwari

Abuja – Majalisar dattawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Majalisar ta tabbatar da su ne a ranar Laraba, 9 ga watan Maris, bayan duba rahoton kwamitin majalisar kan yaki da rashawa da laifukan da suka shafi kudi, jaridar Punch ta rahoto.

Sabbin kwamishinonin da aka tabbatar sun hada da:

1. Sanata Anthony Agbo

2. Anne Otelafu Odey

3. Alhaji Goni Ali Gujba

4. Dr. Louis Solomon Mandama

5. Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya).

Buhari ya janye suna daya sannan ya maye gurbinsa da wani

A jawabinsa, shugaban kwamitin, Sanata Suleiman Abdu Kwari, ya tuna cewa shugaba Buhari ya janye sunan daya daga cikin zababbun kwamishinonin, Misis Mojisola Yaya-Kolade sannan ya maye gurbinta da Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya), wanda kwamitin ya tantance.

Ya bayyana cewa zababbun kwamishinonin sun bayar da amsa yadda ya kamata yayin amsa tambayoyin kwamitin kan yadda za su cika aikin hukumar.

Ya kara da cewa, bayan bincikar takardunsu, kwamitin ya gamsu da cewa wadanda aka zaba suna da kwarewa, mutunci kuma za su iya sauke ayyukan da aka zabe su suyi.

Ya kuma bayyana cewa, babu wani rahoto na tsaro ko korafe-korafe da aka yi kan wani daga cikin wadanda aka nada.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *