play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

Siyasa

Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

Bashir Sani March 9, 2022 19


Background
share close
  • Hukumar zabe INEC tace har yanzun ba ta samu sahihin kwafin takardar hukuncin Kotu na tsige gwamna Umahi ba
  • Kwamishinan INEC na kasa ya ce da zaran sun samu takardar daga Kotu, za su kira zama domin nazari kanta
  • Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta kwace kujerar gwamna da kuma mataimakinsa na jihar Ebonyi kan sauya sheka

Abuja – Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC tace har yanzun ba ta samu kwafin takardar hukuncin da babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yanke kan Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa ba.

Festus Okoye, Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin tara bayanai, ne ya faɗi haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Abuja. Premium Times ta rahoto Mista Okoye na cewa INEC zata zauna kan lamarin da zaran ta karbi takardar hukuncin da Kotu ta yanke.

Hukumar zabe INEC ta faɗi matakin da zata dauka kan gwamnan APC da Kotu ta tsige

“Har yanzun ba’a aiko mana da kwafin hukuncin da ake cewa Kotu ta yanke ba. INEC zata zauna ta yi nazari da zaran an miƙa mata takardar hukuncin Kotu ta gaske.”

Ko wane hukunci Kotu ta yanke?

A ranar Talata, babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Ekwo, ta umarci gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya fice da ofis ɗin gwamna kan sauya shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.

A hukuncin da Alkalin Kotun ya yanke, ya kuma umarci Mista Igwe da ya daina nuna kansa a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ebonyi.

Mai Shari’a Ekwo, ya bayyana cewa tun da sun fice daga PDP, jam’iyyar da mutane suka zabe su karkashinta, kama ta ya yi mutanen biyu su yi murabus daga kan mukamanssu.

Ya kuma ƙara da cewa saɓa wa doka ne ɗan takarar da aka zaɓe shi a wani muƙami karkashin jam’iyyar siyasa kuma ya koma wata jam’iyya ta daban.

Ya ce kuri’un da gwamna Umahi ya samu a zaben 9 ga watan Maris, 2019 na jam’iyyar PDP ne ba na APC ba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *