Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasar na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Naija.
A bayanin da ya sa tare da hotuna a shafinsa na tuwita Atikun, ya kuma ziyarci gwamnan jihar Abubakar Sani Bello.
Duk da kalaman da wasu ke yi na cewa ya je kamun kafa ne da Babangida, a shirinsa na neman sake tsayawa takarar shugaban kasar a 2023, Wazirin na Adamawa a hirarsa da manema labari bayan ziyarar ya ce jajen hare-haren ‘yan fashin daji ya je.
Ziyarar tasa ta kasance daya daga cikin abubuwan da ake ta tattaunawa a shafin tuwita a Najeriyar a yau.
Kotun majistaren dake zamanta a jihar Kano ta sake dage zaman sauraron karar kisan Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar da ake zargin shugaban makaranta ya hallaka kwanaki. Kotun ta bada umurnin cigaba […]
Post comments (0)