play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Shugaba Buhari ya sa hannu a biya tsofaffin Ma’aikata kudin fansho da su ke bi bashi

Siyasa

Shugaba Buhari ya sa hannu a biya tsofaffin Ma’aikata kudin fansho da su ke bi bashi

Bello Sani July 1, 2021 15


Background
share close

Jaridar This Day ta kawo labari cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da rokon da hukumar fansho ta kasa watau PenCom ta gabatar a gabansa.

Hukumar PenCom ta bukaci a ba ta dama ta biya bashin kudin da tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya su ke bi bashi a karkashin tsarin fanshon CPS na kasa.

A wani jawabi da PenCom ta fitar a ranar Laraba, ta ce an ware kudin da za a biya mutane hakkinsu.

Hukumar ta ke cewa za ta biya wadanda su ka yi ritaya daga gwamnatin tarayya ba tare da sun karbi fansho da kudin sallama ba, da kudin wadanda su ka rasu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma amince da biyan karin kudin da aka yi a kan tsarin mafi karancin albashi, wanda wannan canji ya sa fanshonsu ya karu.

A shekarar da ta wuce ne gwamnatin tarayya ta kawo sabon tsarin albashi inda kowane ma’aikaci ya koma tashi da akalla N30, 000, a maimakon N18, 000.

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto, za a fara biyan wadanda su ka yi ritaya daga aiki daga Yulin 2014 da 10% na abin da suka tara a asusun fanshonsu.

“An ware kudin da za a fitar domin a biya mutanen nan hakkokinsu. An zuba kudi a asusun ajiyar fansho na RSA na tsofaffin ma’aikatan da za a biya fanshonsu.”

“Ba da dadewa ba za a sanar da wadannan tsofaffin ma’aikata wadanda kudinsu yake hannunsu.”

Jaridar ta ce hakan na zuwa ne bayan hukumar fanshon PTAD ta karbo fam Euro miliyan £26.5 daga Birtaniya, Wannan kudi sun kai Naira biliyan 13 a kudin gida.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya koka da cewa Hukumar JAMB ta na kawo wasu sharudan shirme da ke sa mutane a wahala, ya ba gwamnatin tarayya shawara.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *