Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwar al’umar Musulmi game da kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW da ake zarginsa da yi yana mai cewa “ba a fahimce ni ba” ne.Kipp
Cikin wani saƙon sauti, an ji malamin na cewa “idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni da na gaggauta tuba”.
Ya ƙara da cewa: “Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin wsaɗncen litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al’umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su.”
BBC Hausa ta fahimci cewa shehin malamin ya nemi afuwar ce bayan wasu ɗalibansa sun nemi ya yi hakan.
Post comments (0)