
Petroleum Industry Bill: Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan rusa NNPC
Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da matakin rusa kamfanin mai na Najeriya, NNPC, muhawara ta ɓarke a tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin matakin ya dace […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata a majalisar dattawan Najeriya, Rochas Okorocha, ya zargi yan siyasar kasar da hannu a tabarbarewar al’amura da rashin hadin kai a tsakanin ‘yan kasar.
Sanata Rochas ya ce rashin bai wa masu kishin kasa damar mulkar kasar na daga cikin dalilan da suka sanya ake samun karuwar masu neman a raba kasar.
A yayin tattaunawarsa da BBC Hausa a Kano, ya ce idan har ‘yan siyasa suka yadda da za su samar da hadin kai a tsakanin jama’a, to kuwa za a cimma manufa, sai dai hakan abu ne mai wahala domin yawancinsu kansu kawai suke tunani ba jama’a ba.
A cewarsa: “Mu muka janyo matsaolin da ake ciki a kasar nan ba kowa ba, a yanzu ‘yan siyasa na yi ne domin cimma bukatun kansu, yawancin wadanda ke neman shugabanci dama suke nema su yi abun da suke nema a kan mulki.”
Ya kuma zargi irin wadannan ‘yan siyasa da nuna bangaranci da kuma siyasar kabilanci, ga kuma uwa uba maganar addini da ake amfani da ita wajen kara raba kan al’umma.
Sanatan ya kara da cewa hanya daya tilo da za a iya magance wannan matsala ita ce wayar da kan ‘yan Najeriya, ta yadda za su fahimci irin kutunguilar da ake shiryawa da kuma manufar yin hakan.
”Matsalar ita ce ba su gane ba ne, idan aka ganar da su za su fahimci cewa irin wadannan matsaloli ne suka hana Najeriya ci gaba, su suka haifar da rashin aikin yi da talauci da kuma siyasar kisa da cutar da jama’a,” in ji shi.
Rashin tafiya da matasa
Jigon na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya jaddada bukatar da ke akwai ta ganin an janyo matasan kasar a jika, ta yadda za a ba su dama su nuna bajintarsu a bangarorin shugabanci, ta yadda ba za su bayar da kunya ba duk lokacin da aka sakar musu ragama.
”Duk matsalar rashin tsaron da ke faruwa a Najeriya za ka ga cewa matasa ne ke haifar da ita, babu wanda ba matashi ba a cikinsu, tun daga kan maganar IPOB, da Boko Haram da ‘yan bindigar nan, za ka ga duk su ne, idan ma ka ji an ce an sace akwatun zabe za ka ga matasan ne dai, ba sa wuce shekaru 40 zuwa kasa,” a cewar Rochas.
Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da matakin rusa kamfanin mai na Najeriya, NNPC, muhawara ta ɓarke a tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin matakin ya dace […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)