Real Madrid za ta kakar bana ta La Liga da wasa a waje a karshen makon 14 ko kuma 15 ga watan Agustan 2021.
Bayan da aka fitar da jadawalin kakar 2021/22 ranar Laraba, Real za ta fara wasan farko a gidan Alaves.
Real za ta karkare kakar da za mu shiga da wasan da za ta buga da Real Betis, karawar mako na 38 kenan ranar 21 ko kuma 22 ga watan Mayun 2022.
Haka kuma za ta fara buga El Clasico a wasan mako na 10 ranar 23 ko kuma 24 ga watan Oktoba a gidan Barcelona wato a Camp Nou.
Za kuma ta karbi bakuncin wasa na biyu na El Clasico da Barcelona a karawar mako na 29 ranar 19 ko kuma 20 ga watan Maris din 2021.
Haka kuma wasan hamayya na birnin Madrid za a yi ne a fafatawar mako na 17 a gidan Real Madrid ranar 11 ko kuma 12 ga watan Disambar 2021.
Atletico Madrid wadda ta lashe La Liga da aka kammala za ta karbi bakuncin wasa na biyu na hamayya da Real Madrid a gumurzun mako na 35 ranar 7 ko kuma 8 ga watan Mayun 2022.
Jadawalin wasannin La Ligar da za a fara karawar farko ta bambanta a wasannin zagaye na biyu, kenan wadanda suka fara haduwa a wasan farko ba a jere za su sake karawa a zagaye na biyu ba.
Post comments (0)