play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Rawar da jama’in tsaro mata suke takawa wajen samar da tsaro a Najeriya

Labarai

Rawar da jama’in tsaro mata suke takawa wajen samar da tsaro a Najeriya

Bello Sani July 5, 2021 12


Background
share close

Sojoji mata na cikin rundunonin tsaro na Najeriya da ke yaƙi da ƴan fashi a arewa maso yammaci da kuma mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.Elo

Mata ƴan sa-kai sun bayar da gundumuwa da taka rawa ga magance wasu daga cikin matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

A watan Janairu ne aka baza sojoji mata 300 a hanyar Abuja zuwa Kaduna domin taimaka wa ayyukan tsaro musamman yaƙi da ƴan fashi masu satar mutane domin kuɗin fansa.

Ana ganin an tura mata fagen daga ne saboda yawan matsalolin tsaron da ke addabar kusan sassan Najeriya.

Masana na ganin jami’an tsaro mata suna tasiri sosai wajen magance matsalolin tsaro musamman rawar da suke taka wa wajen daƙile hare-haren ƙunar bakin wake da ake amfani da mata da kuma bayar da tsaro ga makarantu inda satar ɗalibai ta zama ruwan dare.

Sannan kuma masanan na ganin mata sun ƙware a wajen sasanta tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna.

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, abin da ya sa gwamnatin tarayya ke kira ga ‘yan ƙasa baki ɗaya da su bayar da tasu gudunmawar a harkar tsaro.

Gwamnoni suna ganin akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta nemi taimako daga dakaru na ƙasashen waje ko kuma sojojin haya don yaƙar ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.

Baya ga tashin hankali da ke faruwa sakamakon ayyukan masu neman ɓallewa daga ƙasar a yankin kudu maso gabas, akwai kuma hare-haren ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da faɗan ƙabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya a sauran yankuna.

Yayin da duk wannan ke faruwa, mata da yara ƙanana ne suka fi shiga halin ƙunci. To ko wace irin rawa matan ke takawa game da ayyukan kyautata tsaro a Najeriya?

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *