
Tsadar kayan abinci: ‘Ƴan Najeriya za su ci gaba da ɗanɗana tsadar rayuwa’
Masana tattalin arziki a Najeriya na gargaɗin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi, cewa hauhawar farashin kaya da ake […]
Tarihin Garin Kadawa
Bello Sani
Sarkin Noman Daura Bello Sani
Masarautar Daura Bello Sani
Sauraremu Kai Tsaye Bello Sani
Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da matakin rusa kamfanin mai na Najeriya, NNPC, muhawara ta ɓarke a tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin matakin ya dace yayin da wasu ke sukarsa.
Gwamnatin Najeriya ta ce za a rusa babban kamfanin na kasar NNPC a cikin sauye-sauyen da za a iya wa fannin man kasar karkashin sabuwar dokar inganta harkokin man fetur. Sai dai ya ce za a maye gurbinsa da wani kamfanin mai zaman kansa.
Wannan na daga cikin ayukkan da aka ɗorawa kwamitin share fage kan aiwatar da dokar da Shugaban Buhari ya sanar da kafawa a ranar Alhamis yayin taron majalisar ministoci na mako-mako.
Fitar da sanarwar ke da wuya, ƴan ƙasar suka fara ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta musamman saboda ƴan Najeriya da dama na ganin cewa kusan irin wannan matakin ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar ya ce zai ɗauka idan aka zaɓe shi a lokacin yaƙin neman zaɓensa a 2019.
A cikin manufofinsa da ya bayyana, Atiku ya ce idan ƴan Najeriya suka zaɓe shi zai sayar da kamfanin NNPC ga ƴan kasuwa masu zaman kansu don inganta ɓangaren mai.
A wancan lokacin, waɗannan kalamai sun jawo wa Atiku zagi musamman daga magoya bayan jam’iyyar APC inda suka riƙa ganin hakan a matsayin gurguwar manufa ko kuma wani salo na yin almundahana.
Sai dai yayin da ƴan ƙasar ke ta muhawarar kan wannan mataki, masana a Najeriyar na ci gaba da tsokaci kan matakin na Shugaba Buhari.
Dokta Abdullahi Adamu, malami a jami’ar Baze da ke Abuja kuma masanin harkar makamashi a Najeriya ya ce matakin shugaba Muhammadu Buhari zai amfani ƙasar sosai.
“Idan ka duba kamfanin NNPC yanzu yana da rassa da dama, wasu rassan ma ba dole ne a ce sun tsaya da kansu ba kamata ya yi a ce suna cikin wata ma’aikata guɗa daya amma sai ka ga suna cin gashin kansu,” a cewarsa.
“Hakan ya sa ana kashe kuɗaɗe da yawa wurin kula da waɗannan rassa, shi ya sa aka ce su zo su haɗe a wuri guda a wasu ma’aikatu tsiraru,” in ji Dokta Abdullahi Adamu.
Ya kuma ce an samar da wasu hukumomi guda biyu da za su riƙa kula da harkokin da suka shafi ɓangaren tono da samar da man fetur da iskar gas.
Ya ce wannan zai sauƙaƙa gudanar da shugabanci da kula da harkar mai a ƙasar.
“Ita NNPC a ɓangare guda za a sake shi ya zama kamfani mai zaman kansa, za a ba shi kuɗin sallama a matsayin jari wanda zai kafa sana’o’in da zai yi da zuba hannun jarin da zai riƙa yi musamman a harkar tonon man fetur da samar da shi,” in ji masanin.
Ya bayyana cewa NNPC zai riƙa aiki kaman kamfani mai zaman kansa wanda ya ke neman ya ci riba. Ya ce kuma duk ribar da kamfanin zai samu zai riƙa bai wa gwamnatin tarayya ne don amfanin talaka.
Masanin ya sanar da cewa za a mayar da sunan kamfanin NNPC zuwa NNPC Limited kuma za a ba shi damar bude hannun jari yadda wasu yan Najeriya da ma ƴan ƙasashen waje za su iya siyan hannayen jarin kamfanin.
Haka kuma, ya ce sauya fasalin NNPC ɗin ba zai shafi ma’aikatan kamfanin ba, wato sabanin yadda wasu ke ganin za a kori wasu ma’aikatan kamfanin.
Ya ce “Babu fargabar cewa za a kori mutane daga aiki amma ana iya sauyawa wasu muƙamai ko a cire su a tsarin NNPC ɗin idan aka lura cewa wasu ba a buƙatarsu a wani wuri.”
A farkon makon nan ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu kan sabuwar dokar ta man fetur ta PIB.
Masana tattalin arziki a Najeriya na gargaɗin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi, cewa hauhawar farashin kaya da ake […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)