Mai Shari’a ta Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja, Binta Murtala Nyako, ta ɗage shari’ar jagoran masu rajin kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu zuwa ranar 21 ga watan Oktoba mai zuwa.
A ranar Litinin din nan ne aka so ci gaba da sauraron shari’ar Mr Kanu.
Sai dai rashin kai shi kotun daga bangaren jami’an tsaro ya sa an ɗage shari’ar.
A ƙarshen watan jiya ne, Kotun Tarayya ta bayar da umarnin tsare jagoran ‘yan a-waren, bayan masu gabatar da ƙara sun sake gurfanar da shi gabanta, bayan da aka kamo shi a ƙasar waje.
Gwamnatin Najeriya na tuhumarsa da laifuka 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta’addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma kokarin tunzura jama’a don haifar da yamutsi.
Lauyoyin gwamnati da na jagoran ‘yan a-waren sun hallara a kotun ko da yake wakilin BBC da ke kotun ya ce an hana wasu lauyoyi da ke wakiltar kungiyoyin kabilar Igbo shiga cikinta.
Wasu masu fafutuka a ƙasar sun yi gangamin goyon bayan Nnamdi Kanu a kofar babbar kotun.
Sai dai bayanai sun nuna cewa ‘yan sanda sun kama masu zanga-zanga akalla bakwai.
Ran mai shari’a ya ɓaci
A zaman kotun na ranar Litinin, mai shari’a Binta Murtala Nyako, ta bayyana bacin ranta bisa rashin gabatar da Mr Kanu.
Ta yi gargadin cewa ba za ta sake yarda da halin da aka nuna na kin gabatar da shi a gaban kotu ba.
Tun da farko, lauyan Mr Kanu Barrister Ifeanyi Ejiofor, ya yi korafin cewa hukumomin kasar sun ki barinsu su gana da mutumin da ake tuhuma.
Akarshen watan Yuni ne ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami, ya sanar da kama Mr Kanu, wanda ya tsere daga kasar.
Zuwa yanzu hukumomin Najeriya ba su bayyana kasar da aka kama jagoran ‘yan a-waren na Biafra ba, sai dai kamfanin dillacin labarai na kasar ya ce wani karamin minista a ofishin harkokin wajen Birtaniya ya bukaci Najeriya ta yi musu bayani a kan hakan.
Shi dai Lauyan da ke kare Nnamdi Kanu ya ce an kama shi ne a Kenya, kuma an azabtar da shi tsawon kwana takwas kafin a mika shi ga hukumomin Najeriya.
Ofishin jakadancin Kenya a Najeriya ya musanta wannan zargi, sai dai kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra ta dage a kan haka
Ganduje ya yi magana kan shari’ar Sheikh Abduljabbar Gwamnan Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta bibiyi batun Sheikh Abduljabbar Kabara “har zuwa karshensa.” Mai […]
Post comments (0)