play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Muhuyi Magaji: Wane ne shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano da aka dakatar?

Siyasa

Muhuyi Magaji: Wane ne shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano da aka dakatar?

Bello Sani July 5, 2021 7


Background
share close

Majalisar Dokokin Jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta dakatar da shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da cin hanci da rashawa ta jihar KPCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, na tsawon wata guda.

A zaman da ta yi a ranar Litinin ne majalisar ta ce ta dakatar da Muhuyi, saboda wani ƙorafi da ta samu a kansa daga ofishin Babban Akanta na jihar ta Kano.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano Labaran Abdul Madari ya shaida wa BBC cewa an dakatar da Muhyi Magaji ne saboda ƙin amincewa da akawun da aka aika masa daga ofishin babban akawun jihar.

Sai dai Muhuyi ya yi watsi da wannan zargi a wata hira da BBC ta yi da shi a baya-bayan nan.

Ana daɗe ana yi wa Muhuyi kallon mutum mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan abubuwa da dama a jihar Kano.

Bari mu ɗan yi waiwaye kan waye Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Wane ne Muhuyi Magaji?

Muhuyi Magaji wani ɗan siyasa ne kuma ɗan gwagwarmaya mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano.

A lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau yayin da Muhuyi yake matsayin mataimakin ƙaramar hukumar Rimin Gado, ya taɓa kai ƙorafi ga hukumar EFCC ta ƙasa kan wasu kuɗaɗen ƙaramar hukumar da suka maƙale.

Bayan kuɗaɗen sun fito ne ya fara gudanar da wasu ayyukan ci gaba da su a ƙaramar hukumar, lamarin da ya ja babu shiri shugaban ƙaramar hukumar ya dawo daga wata tafiya.

Wannan abu ya jawo saɓani tsakaninsa da shugaban ƙaramar hukumar ta Rimin Gado. Lamarin nan ya sake fiddo da Muhuyi a idon al’umma a matsayin mai yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya taba dakatar da rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo a jihar Kano bayan da ya kai ƙorafi kotu, lokacin dai da yake matsayin mataimakin ƙaramar hukumar.

Bayan da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya koma mulki a shekarar 2015, Muhuyi ya zama jami’in ƙaramar hukuma na farko da ya taɓa mayar da motar gwamnati, wanda hakan ya tilasta wa sauran shugabannin ƙananan hukumomi mayar da nasu.

Ya ce ya yi hakan ne don tsayawa a kan gaskiya. Sai dai hakan ya jawo masa matuƙar baƙin jini a wajen takwarorinsa a lokacin.

Ya taɓa kafa ƙungiyar yaƙi da cin hanci da rashawa, kuma bayan nan ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya naɗa shi shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rahswa ta jihar Kano a shekarar 2016.

A lokacin da yake riƙe da wannan muƙami ya janyo ce-ce-ku-ce sosai inda ya dinga rigima da ɓangarori daban-daban.

Ya yi rigima da ma’ikatan kotu, ya binciki alƙalai, ya binciki manya-manyan ƴan siyasa, ya binciki Masarautar Kano har sau biyu duk kan zargin almundahana da ɓarnata kudaɗen gwamnati.

A lokacin da yake shugabantar hukumar ya koma ya yi karatun shari’a inda ya zama lauya.

A yanzu za a zuba a ga mai zai faru tsakanin Muhuyi Magaji da Majalisar Dokokin Jihar Kano

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *