play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Makiyaya basa rike AK-47, sanduna da adduna kadai suke rikewa, in ji Buhari

Labarai

Makiyaya basa rike AK-47, sanduna da adduna kadai suke rikewa, in ji Buhari

Bello Sani June 11, 2021 4


Background
share close

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya bayyana cewa makiyaya a Najeriya basa daukar komai sama da sanduna da adda don tara ciyawar shanun su.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa shugaban a tattaunawarsa da ‘yan jaridu a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya dage cewa makiyaya ‘yan asalin Najeriya basa amfani da manyan makamai kamar AK-47.

Da yake ci gaba da magana, shugaban na Najeriya ya bayyana makiyayan da ke dauke da muggan makamai cewa ba ‘yan Najeriya bane, tabbas daga wasu kasashen suke.

Ya bayyana cewa Fulani daga kasashen Mauritaniya da Afirka ta Tsakiya suna kama da juna, ya kara da cewa mutane galibi suna yi musu kallon su ‘yan Najeriya ne, P.M News ta ruwaito shi yana cewa.

Buhari ya ce:

“Mai kiwon shanu na Najeriya ba zai dauki komai sama da sanda ba… wani lokacin kuma adduna don sare wasu bishiyoyi.”
“Amma wadancan gogaggu wadanda suke dauke da AK-47… a duk yankin Sahel, mutane suna garzayowa zuwa Najeriya. Ku sani, Fulani daga Mauritaniya da Afirka ta Tsakiya kamarsu daya. Don haka suna ganin su ‘yan Najeriya ne.”

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su daina jiransa don warware duk wata matsala da suke fuskanta, yana mai cewa ya kamata su dakatar da kai hare-haren makiyaya a jihohinsu., Sahara Reporters ta ruwaito.

Jihohi da yawa na fuskantar munanan hare-hare kan al’ummomi, inda ake fama da rikici ta fuskoki da dama ciki har da na makiyaya, wanda yasa ake matsa wa Shugaban kasa a matsayinsa na Babban Kwamandan sojin kasar da ya kawo dauki.

Kasancewarsa Bafulatani, da yawa daga yankunan kudancin Najeriya sun zarge shi da nuna son kai da rashin son magance hare-hare daga makiyaya, wadanda kuma galibi Fulani ne.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *