play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Labari da duminsa: Jamhuriyar Benin ta saki Sunday Igboho bayan tsare shi na watanni

Labarai

Labari da duminsa: Jamhuriyar Benin ta saki Sunday Igboho bayan tsare shi na watanni

Bashir Sani March 7, 2022 13


Background
share close

Kwatano, Benin – Jaridar Punch ta rahoto cewa, Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki dan dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho bayan doguwara tsarewa da ya sha.

Hadin kan Yarbawa a kungiyoyin rajin kare hakkin Yarabawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta Saki Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran’. Har yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai game da sakin Sunday Igboho da ke tsare a Jamhuriyar Benin tun shekarar 2021.

Idan baku manta ba, an tsare Sunday Igboho ne tun bayan da ya yi kokarin guduwa Turai yayin da gwamnatin Najeriya ta ayyana nemansa ruwa a jallo.

Karin bayani na nan tafe…

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *