safiyar ranar Arfa ne ake gagarumin aikin sauya rigar dakin Ka’aba a birnin Makka na kasar Saudiyya, wanda ake yi sau daya a kowace shekara, kodayake na wannan shekarar an sauya shi tun ranar Lahadi 8 ga Zul Hijjah.i
Ana wannan aikin ne a lokacin da alhazai suka bar birnin Makka suke tsayuwar Arfa, wadda ita ce babban rukunin aikin Hajji.
Sabon abin da alhazai za su tarar idan suka koma Makka ranar Babbar Sallah shi ne sabuwar rigar Ka’aba.
Ana ɗaukar sauya wa Ka’aba riga a matsayin wani babban lamari na girmama ɗakin na Allah da kuma tsarkake shi.
Sauya rigar na daga abubuwa mafiya daɗewa a tarihin duniya. An shafe ɗaruruwan shekaru ana sauya wa Ka’aba riga gabanin zuwan Musulunci, abin da wasu sarakunan Larabawa suka riƙe kuma ya zama wani babban abin alfahari a wajen Larabawa.
A yanzu kimanin ma’aikata 160 ne suke aikin sauya rigar ta Ka’aba a duk shekara.
Saka sabwar riga ga kofar Ka’aba shi ne abin da ya fi komai wahala a wajen sauya rigar, kasancewar yadda ake ɗinka rigar kofar ya bambanta da sauran tufafin da ake sakawa a jikin bangon ɗakin.
Post comments (0)